9 Da Yowab ya ga an ja masa dāgar yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu Isra'ilawa, ya sa su gabza da Suriyawa.
10 Sauran mutane kuwa ya sa su a hannun Abishai, ƙanensa. Ya sa su gabza da Ammonawa.
11 Ya ce musu, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, ku kawo mini gudunmawa, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinku, sai in kai muku gudunmawa.
12 Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”
13 Sa'an nan Yowab da mutanensa suka matsa, su gabza da Suriyawa. Suriyawa kuwa suka gudu.
14 Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.
15 Sa'ad da Suriyawa suka ga Isra'ilawa sun ci su, suka tattara kansu.