4 Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo 'yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”
5 Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa.
6 Sai kuma ya biya diyyar 'yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”
7 Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra'ila, na cece ka daga hannun Saul.
8 Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra'ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.
9 Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.
10 Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.