23 Dukan ƙasar ta yi ta kururuwa sa'ad da mutane suka tashi. Sarki ya haye rafin Kidron, mutane kuma suka haye, suka nufi jeji.
24 Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin.
25 Sa'an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa.
26 Amma idan Ubangiji bai ji daɗina ba, to, ga ni, sai ya yi yadda ya ga dama da ni.”
27 Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.
28 Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”
29 Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.