12 Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.”
13 Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature.
14 Sarki da dukan jama'ar da suke tare da shi suka isa Urdun a rafke. Sai suka shaƙata.
15 Absalom kuwa ya zo Urushalima tare da dukan mutanen Isra'ila da suke tare da shi. Ahitofel kuma yana tare da shi.
16 Sa'ad da Hushai Ba'arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”
17 Sai Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake yi wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
18 Hushai ya amsa, ya ce, “Ba haka ba, ni dai zan zama na wanda Ubangiji, da wannan jama'a, dukan mutanen Isra'ila suka zaɓa. Zan zauna tare da mutumin da aka zaɓa.