2 Zan fāɗa masa sa'ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya, in firgitar da shi. Dukan mutanen da suke tare da shi za su gudu. Shi kaɗai zan kashe.
3 Zan kawo maka dukan jama'a kamar yadda akan kawo amarya a gidan angonta. Ran mutum guda kaɗai kake nema, sauran mutane duka kuwa su yi zamansu lafiya.”
4 Wannan shawara ta gamshi Absalom da dattawan Isra'ila.
5 Sa'an nan Absalom ya ce, “A kirawo Hushai Ba'arkite don mu ji abin da shi kuma zai faɗa.”
6 Da Hushai ya zo, sai Absalom ya ce masa, “Ga shawarar da Ahitofel ya bayar, mu bi ta? Ko kuwa? Kai, me ka ce?”
7 Sai Hushai ya ce wa Absalom, “A wannan lokaci dai shawarar da Ahitofel ya bayar ba ta da kyau.”
8 Hushai ya ci gaba da cewa, “Ka san tsohonka da jama'arsa jarumawa ne, yanzu a husace suke kamar damisar da aka kwashe wa 'ya'ya a jeji. Tsohonka kuma ya ƙware da sha'anin yaƙi, ba tare da mutanensa zai kwana ba.