1 Aka faɗa wa Yowab, cewa, sarki yana kuka, yana makoki domin Absalom.
2 Saboda haka sai nasarar da aka ya a ranar ta zama makoki ga jama'a duka, gama jama'a suka ji an ce sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.
3 Sojojin suka shiga birni sururu kamar waɗanda sukan shiga birni a ɓoye da kunya saboda sun gudu daga wurin yaƙi.
4 Sarki ya rufe fuskarsa, ya yi kuka da ƙarfi, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ya Absalom, ɗana, ɗana!”
5 Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan 'ya'yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka.
6 Gama kana ƙaunar maƙiyanka, amma kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Gama yau ka bayyana a fili, shugabannin sojojinka da fādawanka ba a bakin kome suke a gare ka ba. Gama yau na gane da a ce Absalom yana da rai, mu kuwa muka mutu duka, da daɗi za ka ji.