30 Mefiboshet ya ce wa sarki, “A ma bar masa duka ya mallaka, ni dai tun da ubangijina, sarki, ya komo gida lafiya, to, alhamdu lillahi.”
31 Barzillai Bagileyade kuma ya gangara daga Rogelim zuwa wurin sarki domin ya yi wa sarki rakiya zuwa hayin Urdun.
32 Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa'ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne.
33 Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka zo mu tafi tare zuwa Urushalima, ni kuwa zan riƙa biya maka bukata.”
34 Amma Barzillai ya amsa, ya ce, “Shekaruna nawa suka ragu har da zan tafi Urushalima tare da sarki?
35 A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe.
36 Ban cancanci wannan irin babban lada ba. Zan dai yi maka 'yar rakiya zuwa hayin Urdun.