7 Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”
8 Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim.
9 Ya naɗa shi Sarkin Gileyad, da Ashiru, da Yezreyel, da Ifraimu, da ƙasar Biliyaminu, da dukan Isra'ila.
10 Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba'in sa'ad da ya ci sarautar Isra'ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda.
11 Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.
12 Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.
13 Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin.