39 Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba,Suna kwance warwar a ƙafafuna.
40 Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi,Nasara kuma a kan abokan gābana.
41 Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana,Na hallaka waɗanda suke ƙina.
42 Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su,Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.
43 Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.
44 “Ka cece ni daga jama'ata mai tawaye,Ka sa in yi mulkin al'ummai,Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.
45 Baƙi sun zo suna rusuna mini,Sa'ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.