43 Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.
44 “Ka cece ni daga jama'ata mai tawaye,Ka sa in yi mulkin al'ummai,Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.
45 Baƙi sun zo suna rusuna mini,Sa'ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.
46 Zuciyarsu ta karai,Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.
47 “Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa!Allah ne ƙaƙƙarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa!
48 Ya ba ni nasara a kan abokan gabana,Ya sa mutane a ƙarƙashin mulkina,
49 Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiya.Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan maƙiyana,Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali.