16 Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, 'yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci.
17 Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suka ajiye shi a wurinsa a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa dominsa. Dawuda ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama a gaban Ubangiji.
18 Sa'ad da ya gama miƙa hadayun ƙonawa da na salama, sai ya sa wa mutanen albarka da sunan Ubangiji Mai Runduna.
19 Ya kuma rarraba wa dukan taron jama'ar Isra'ila, mata da maza, ƙosai, da nama, da zabibi, sa'an nan dukan mutane suka watse, kowa ya tafi gidansa.
20 Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, 'yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra'ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”
21 Sai Dawuda ya ce wa Mikal, “Ai, na yi wannan a gaban Ubangiji wanda ya zaɓe ni a madadin mahaifinki da iyalinsa, ya naɗa ni in zama Sarkin Isra'ila, wato jama'ar Ubangiji. Lalle zan yi rawar farin ciki a gaban Ubangiji.
22 Zan mai da kaina abin raini fiye da haka, zan kuma zama abin raini gare ki, amma barori mata da kika ambata, za su girmama ni.”