2 Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.
3-4 Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Suka sa akwatin alkawari a sabuwar karusa. Uzza da Ahiyo, 'ya'yan Abinadeb, maza, suka bi da karusar da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo ne yake tafiya a gaban akwatin alkawarin.
5 Sai Dawuda da Isra'ilawa duka suka yi rawa sosai don farin ciki a gaban Ubangiji. Aka yi ta raira waƙoƙi, ana kaɗa molaye, da garayu, da goge, da kacakaura, da kuge.
6 Da suka zo masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa ya riƙa akwatin alkawarin Allah, gama takarkaran sun yi kwarangyasa.
7 Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari.
8 Sai Dawuda ya ji haushi domin Ubangiji ya fashe haushinsa a kan Uzza. Aka sa wa wurin suna Feresauzza har wa yau.
9 Dawuda kuwa ya ji tsoron Ubangiji a ran nan, ya ce, “Ƙaƙa zan ajiye akwatin alkawarin Ubangiji a wurina?”