9 Sa'an nan sarki ya aiki shugaba tare da mutum hamsin su taho da Iliya. Mutumin kuwa ya haura wurin Iliya a kan dutse, ya ce masa, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko.”
10 Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.
11 Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba tare da mutum hamsin. Suka tafi, shugaban ya ce wa Iliya, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko da sauri.”
12 Iliya kuwa ya ce musu, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka guda hamsin.” Wuta kuwa daga wurin Allah ta sauko daga sama ta cinye shugaban da mutanensa hamsin.
13 Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba, na uku ke nan, tare da mutanensa hamsin. Sai shugaba na uku ya tafi ya rusuna a gaban Iliya, ya roƙe shi, ya ce, “Ya mutumin Allah, ina roƙonka ka ga darajar raina da na barorinka, su hamsin.
14 Gama wuta ta sauko daga sama ta cinye shugabanni biyu tare da mutanensu hamsin hamsin, amma ka dubi darajar raina.”
15 Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Ka sauka, ka tafi tare da shi, kada ka ji tsoronsa.” Iliya kuwa ya tashi, ya tafi tare da shi har gaban sarki.