1 Ahab yana da 'ya'ya maza saba'in a Samariya, sai Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika zuwa Samariya wurin shugabanni da dattawan birni, da masu lura da 'ya'yan Ahab.
2 Ya ce, “Yanzu dai, da zarar wasiƙun nan sun iso wurinku, da yake kuke lura da 'ya'yan Ahab, kuna kuma da karusai, da dawakai, da kagara, da makamai,
3 sai ku zaɓi wanda ya fi dacewa duka daga cikin 'ya'yan Ahab, ku naɗa shi sarki, ku yi yaƙi, domin ku tsare gidan Ahab.”
4 Amma suka ji tsoro ƙwarai, suka ce, “Ga shi, sarakuna biyu ba su iya karawa da shi ba, balle mu.”