20 Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba'al. Aka kuwa kira taron,
21 sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan.
22 Sa'an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin.
23 Bayan wannan Yehu ya shiga haikalin Ba'al tare da Yehonadab ɗan Rekab, ya ce wa masu yi wa Ba'al sujada, “Ku bincike, ku tabbata, ba wani bawan Ubangiji tare da ku, sai dai masu yi wa Ba'al sujada kaɗai.”
24 Sa'an nan Yehu da Yehonadab suka shiga don su miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Yehu ya riga ya sa mutum tamanin a waje, ya ce musu, “Mutumin da ya bar wani daga cikin waɗanda na bashe su a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”
25 Nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya ta ƙonawa, sai ya ce wa mai tsaro da shugabannin, “Ku shiga, ku karkashe su, kada ku bar wani ya tsere.” Da suka karkashe su, sai suka fitar da su waje, sa'an nan suka shiga can cikin haikalin Ba'al.
26 Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su.