1 Sa'ad da Ataliya, uwar Ahaziya, ta ga ɗanta ya rasu, sai ta tashi ta hallaka dukan 'ya'yan sarauta.
2 Amma Yehosheba 'yar sarki Yoram, 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba.
3 Ya zauna tare da ita shekara shida a ɓoye, a cikin Haikalin Ubangiji sa'ad da Ataliya take mulkin ƙasar.
4 A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya aika ya kawo shugabannin Keretiyawa da na masu tsaro a Haikalin Ubangiji. Ya yi alkawari da su, ya sa suka yi rantsuwa a Haikalin Ubangiji, sa'an nan ya nuna musu ɗan sarki.
5 Ya kuma umarce su cewa, “Abin da za ku yi ke nan, sai sulusinku da sukan zo aiki a ranar Asabar, su yi tsaron gidan sarki.
6 Sulusinku kuma zai kasance a ƙofar Sur. Ɗaya sulusin kuma zai kasance a bayan masu tsaro, haka za ku yi tsaron gidan, ku tsare shi.
7 Ƙungiyarku biyu kuma waɗanda sukan tashi aiki ran Asabar, za su yi tsaron Haikalin Ubangiji da kuma sarki.