9 Shugabannin fa suka aikata bisa ga dukan abin da Yehoyada firist ya umarta. Kowa ya zo duk da mutanensa waɗanda za su huta aiki ran Asabar tare da waɗanda za su yi aiki ran Asabar, suka zo wurin Yehoyada.
10 Firist kuwa ya ba shugabannin māsu da garkuwoyin Dawuda waɗanda suke cikin Haikalin Ubangiji.
11 Matsara suka tsaya, kowa da makaminsa a hannu, daga wajen kudu na Haikalin zuwa wajen arewa. Suka kewaye bagade da Haikali.
12 Sa'an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa'an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”
13 Da Ataliya ta ji muryoyin matsara da na jama'a, sai ta zo wurin mutane a Haikalin Ubangiji.
14 Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”
15 Yehoyada, firist kuwa, ya umarci shugabannin sojoji, ya ce, “Ku fitar da ita daga nan, duk kuma wanda yake son kāre ta, ku sa takobi ku kashe shi.” Ya kuma ce, “Kada a kashe ta a Haikalin Ubangiji.”