8 Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
9 Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.
10 A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta.
11 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama'ar Isra'ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat.
12 Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfin da ya yi yaƙi da Amaziya Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.2Sar 14.15; 1Sar 15.31
13 Yehowash kuwa ya mutu, aka binne shi a Samariya, inda ake binne sarakunan Isra'ila, sai Yerobowam na biyu ya gāji gadon sarautarsa.
14 Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”