1 A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta.
2 Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Yehowaddin ta Urushalima.
3 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma bai kai kamar kakansa Dawuda ba. Ya yi kamar yadda tsohonsa, Yowash ya yi.
4 Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadaya, da ƙona turare a matsafai na kan tuddai.
5 Sa'ad da mulkin ya kahu sosai a hannun Amaziya, sai ya kashe fādawan da suka kashe tsohonsa.
6 Amma bai kashe 'ya'yan masu kisankai ɗin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”
7 Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa'an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.