1 A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam na biyu Sarkin Isra'ila, Azariya ɗan Amaziya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
2 Yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara hamsin da biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa, Yekoliya ta Urushalima.
3 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda Amaziya, tsohonsa, ya yi.
4 Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai.