29 Amma duk da haka kowace al'umma ta riƙa yin gumakanta, tana ajiye su a wuraren yin tsafin na kan tuddai waɗanda Samariyawa suka gina. Kowace al'umma kuma ta yi haka a garin da ta zauna.
30 Mutanen Babila suka yi Sukkot-benot, mutanen Kuta suka yi Nergal, mutanen Hamat suka yi Ashima.
31 Awwiyawa suka yi Nibhaz da Tartak, mutanen Sefarwayim suka miƙa 'ya'yansu hadaya ta ƙonawa ga Adrammelek da Anammelek, gumakansu.
32 Su ma suka yi tsoron Ubangiji, suka sa mutane iri dabam dabam su zama firistocin wuraren tsafinsu na kan tuddai. Firistocin nan suka miƙa hadayu dominsu a ɗakunan tsafinsu na kan tuddai.
33 Waɗannan mutane su ma suka yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka bauta wa gumakansu ta hanyar da al'umman da aka kwaso su daga cikinsu suke yi.
34 Har wa yau suna yin yadda suka yi a dā. Ba su yi tsoron Ubangiji ba, ba su bi dokoki, ko ka'idodi, ko shari'a, ko umarnan Ubangiji ba, waɗanda ya umarci 'ya'yan Yakubu, wanda ya sa wa suna Isra'ila.
35 Ubangiji ya yi alkawari da 'ya'yan Yakubu, ya kuma umarce su kada su yi wa gumaka sujada ko su durƙusa musu, ko su bauta musu, ko su miƙa musu hadayu.