5 Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra'ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa.
6 Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa.
7 Ubangiji kuwa ya kasance tare da shi, duk inda ya nufa sai ya sami albarka. Ya tayar wa Sarkin Assuriya, ya ƙi bautar masa.
8 Ya kuma bugi Filistiyawa har zuwa Gaza da iyakarta daga hasumiya zuwa birni mai garu.
9 A shekara ta huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, a lokacin Hosheya ɗan Ila, Sarkin Isra'ila, yana da shekara bakwai da sarauta, sai Shalmanesar Sarkin Assuriya ya kawo wa Samariya yaƙi, ya kewaye ta.
10 A ƙarshen shekara ta uku, ya ci ta da yaƙi. A lokacin Hezekiya yana da shekara shida da sarauta, Hosheya kuwa yana da shekara tara da tasa sarauta.
11 Sarkin Assuriya kuwa ya kwashi Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.