16 Sa'an nan Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji abin da Ubangiji ya ce,
17 ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe duk abin da yake cikin gidanka, da abin da kakanninka suka tanada, zuwa Babila.
18 Za a kuma kwashe waɗansu 'ya'yanka da ka haifa zuwa Babila, can za a maishe su babani a fādar Sarkin Babila.’ ”
19 Sarki Hezekiya kuwa ya fahimci za a yi zaman lafiya da salama a zamaninsa, don haka ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”
20 Sauran ayyukan Hezekiya da dukan ƙarfinsa, da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa don ya kawo ruwa cikin birnin, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
21 Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.