1 Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yedida, 'yar Adaya na Bozkat.
2 Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.
3 A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, wato jikan Meshullam, magatakarda, zuwa Haikalin Ubangiji, ya ce,
4 “Ka tafi wurin Hilkiya babban firist domin a lasafta yawan kuɗin da aka kawo cikin Haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tattara daga wurin jama'a.
5 A ba da kuɗin a hannun masu lura da ma'aikata waɗanda suke gyaran Haikalin Ubangiji, su kuma su ba waɗanda suke gyaran Haikalin,
6 wato masu sassaƙa, da magina, domin a sayi katako da dutsen da aka haƙo don gyaran Haikalin.
7 Kada a tambaye su yadda suka kashe kuɗin da aka sa a hannunsu, gama su amintattu ne.”