6 wato masu sassaƙa, da magina, domin a sayi katako da dutsen da aka haƙo don gyaran Haikalin.
7 Kada a tambaye su yadda suka kashe kuɗin da aka sa a hannunsu, gama su amintattu ne.”
8 Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi.
9 Sai Shafan magatakarda ya tafi ya faɗa wa sarki cewa, “Baranka ya kwashe kuɗin da ya tarar a Haikali, na kuwa ba masu lura da ma'aikatan Haikalin Ubangiji.”
10 Ya kuma ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Ya kuwa karanta wa sarki littafin.
11 Sa'ad da sarki ya ji maganar da take cikin littafin dokoki, sai ya kece tufafinsa.
12 Sa'an nan ya umarci Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikaiya, da Shafan magatakarda, da Asaya baran sarki cewa,