17 Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.
18 Nebuzaradan kuma ya tafi da Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofa.
19 Daga cikin birnin kuma ya tafi da wani shugaban sojoji, da 'yan majalisar sarki mutum biyar, da magatakardan shugaban sojoji wanda ya tattara jama'ar ƙasar, da mutum sittin na ƙasar waɗanda aka samu a birnin.
20 Nebuzaradan shugaban sojoji ya kai su wurin Sarkin Babila a Ribla ta ƙasar Hamat.
21 Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can.Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.
22 A kan sauran waɗanda suka ragu a ƙasar Yahuza, waɗanda Sarkin Babila, Nebukadnezzar, ya bari, ya naɗa musu Gedaliya ɗan Ahikam, wato jikan Shafan, ya zama hakiminsu.
23 Sa'ad da shugabannin mayaƙa su da mayaƙansu suka ji Sarkin Babila ya naɗa Gedaliya ya zama hakimi, sai suka zo tare da mutanensu wurin Gedaliya a Mizfa, wato su Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan ɗan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, mutumin Netofa, da Yazaniya mutumin Ma'aka.