7 Aka kashe 'ya'yansa maza a idonsa, sa'an nan aka ƙwaƙule masa idanu, aka kuma ɗaure shi da sarƙa, aka kai shi Babila.
8 A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima.
9 Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.
10 Dukan sojojin Kaldiyawa waɗanda suke tare da shugaban, suka rushe garun da yake kewaye da Urushalima.
11 Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.
12 Amma shugaban sojojin ya bar matalautan ƙasar su zama masu gyaran inabi, da masu noma.
13 Sai Kaldiyawa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalansu, da kwatarniyar ruwa na tagullar da take cikin Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagullar zuwa Babila.