17 Amma macen ta sami juna biyu, ta kuwa haifi ɗa a daidai lokacin da Elisha ya faɗa mata.
18 Da yaron ya yi girma, sai wata rana ya bi mahaifinsa gona zuwa wurin masu girbi.
19 Sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo, kaina, kaina.”Uban kuwa ya ce wa baransa, “Ka ɗauke shi, ka kai shi wurin uwar.”
20 Da aka ɗauke shi, aka kai wa uwar, sai ya zauna a cinyar uwar har rana tsaka, sa'an nan ya rasu.
21 Sai ta hau, ta kwantar da shi a gadon annabi Elisha, sa'an nan ta rufe ƙofa, ta fita.
22 Sa'an nan ta aika a faɗa wa mijinta, ta ce, “Ka aiko mini ɗaya daga cikin barori da jaki domin in tafi wurin annabi Elisha, zan komo da sauri.”
23 Sai ya ce, “Me ya sa za ki tafi wurinsa yau? Ai, yau ba amaryar wata ba ce, ba kuwa ranar Asabar ba ce.”Ita kuwa ta ce, “Ba kome, kada ka damu.”