20 Da aka ɗauke shi, aka kai wa uwar, sai ya zauna a cinyar uwar har rana tsaka, sa'an nan ya rasu.
21 Sai ta hau, ta kwantar da shi a gadon annabi Elisha, sa'an nan ta rufe ƙofa, ta fita.
22 Sa'an nan ta aika a faɗa wa mijinta, ta ce, “Ka aiko mini ɗaya daga cikin barori da jaki domin in tafi wurin annabi Elisha, zan komo da sauri.”
23 Sai ya ce, “Me ya sa za ki tafi wurinsa yau? Ai, yau ba amaryar wata ba ce, ba kuwa ranar Asabar ba ce.”Ita kuwa ta ce, “Ba kome, kada ka damu.”
24 Amma ta yi wa jakin shimfiɗa, ta kuma ce wa baranta, “Yi ta kora mini jakin, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.”
25 Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel.Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.
26 Ruga ka tarye ta, ka tambayi lafiyarta, da ta mijinta, da ta ɗanta.”Ta amsa, ta ce, “Lafiya ƙalau.”