33 Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu'a ga Ubangiji.
34 Sa'an nan ya kwanta a kan yaron, ya sa bakinsa a bakin yaron, ya sa idanunsa a idanun yaron, hannuwansa kuma a kan na yaron, ya miƙe jikinsa akan yaron, sai jikin yaron ya yi ɗumi.
35 Elisha ya tashi, ya yi ta kai da komowa a cikin gidan, sa'an nan ya sāke hawan ɗakin, ya miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu.
36 Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”
37 Ta kuwa zo, ta faɗi a gaban Elisha har ƙasa, sa'an nan ta ɗauki ɗanta, ta fita.
38 Elisha kuwa ya koma Gilgal sa'ad da ake fama da yunwa a ƙasar. Sa'ad da ƙungiyar annabawa suke zaune a gabansa, sai ya ce wa baransa, “Dora babbar tukunya, ka dafa wa annabawan nan fate-fate.”
39 Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo 'ya'yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba.