35 Elisha ya tashi, ya yi ta kai da komowa a cikin gidan, sa'an nan ya sāke hawan ɗakin, ya miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu.
36 Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”
37 Ta kuwa zo, ta faɗi a gaban Elisha har ƙasa, sa'an nan ta ɗauki ɗanta, ta fita.
38 Elisha kuwa ya koma Gilgal sa'ad da ake fama da yunwa a ƙasar. Sa'ad da ƙungiyar annabawa suke zaune a gabansa, sai ya ce wa baransa, “Dora babbar tukunya, ka dafa wa annabawan nan fate-fate.”
39 Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo 'ya'yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba.
40 Amma da suka ɗanɗana, sai suka ta da murya suka ce, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyar nan!” Ba su iya cin abincin ba.
41 Sai Elisha ya ce, “To, ku kawo gari.” Aka kawo masa, ya kuwa zuba garin a tukunyar, sa'an nan ya ce, “Ku kwaso wa mutanen. Yanzu dai kome lafiya.”