16 Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.”Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.
17 Na'aman kuwa ya ce, “Da yake ka ƙi ka karɓa, ina roƙonka, ka ba baranka labtun alfadari biyu na ƙasa, gama nan gaba baranka ba zai ƙara miƙa hadaya ta ƙonawa ko baiko ga wani gunki ba, sai dai Ubangiji.
18 Sai dai Ubangiji ya gafarta mini lokacin da na bi sarki zuwa cikin haikalin Rimmon, gunkin Suriya, don ya yi sujada. Na gaskata Ubangiji zai gafarta mini.”
19 Elisha kuwa ya ce masa, “Ka sauka lafiya.” Na'aman ya tafi.Amma tun Na'aman bai yi nisa ba,
20 sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”
21 Gehazi kuwa ya bi bayan Na'aman.Da Na'aman ya ga wani yana biye da shi a guje, sai ya sauka daga karusarsa, ya juya ya tarye shi, ya ce, “In ce ko lafiya?”
22 Gehazi ya ce, “Lafiya ƙalau, maigidana ne ya aiko ni in faɗa maka, yanzu yanzu waɗansu samari biyu daga ƙungiyar annabawa suka zo wurinsa daga ƙasar tudu ta Ifraimu, yana roƙonka, ka ba ni talanti ɗaya na azurfa da rigunan ado guda biyu in kai masa.”