3 Ɗaya daga cikinsu kuwa ya ce, “In ka yarda, ka tafi tare da mu.”Elisha kuwa ya yarda, ya ce, “To, mu tafi.”
4 Ya kuwa tafi tare da su.Sa'ad da suka isa Urdun, suka sassari itatuwa.
5 Amma sa'ad da ɗaya daga cikinsu yake saran wani gungume, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe ya fāɗa a ruwa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Wayyo, maigida, me zan yi? Abin aro ne.”
6 Sa'an nan Elisha ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?”Da ya nuna masa wurin, sai ya karyi tsumagiya, ya jefa a wurin, ya sa ruwan gatarin ya taso bisa kan ruwan.
7 Sa'an nan ya ce, “Ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu, ya ɗauka.
8 Wata rana, sa'ad da Sarkin Suriya yake yaƙi da Isra'ila, sai ya shawarci fādawansa, suka zaɓi wurin da za su kafa sansani.
9 Amma Elisha ya aika wa Sarkin Isra'ila, ya ce, “Ka yi hankali, kada ka wuce wuri kaza, gama Suriyawa suna gangarawa zuwa can.”