1 Elisha kuwa ya kirawo ɗaya daga cikin annabawa matasa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kurtun mai, ka tafi Ramot-gileyad.
2 Sa'ad da ka isa can, sai ka nemi Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ka shiga, ka sa ya tashi daga wurin abokansa, ka kai shi cikin ɗaki.
3 Sa'an nan ka ɗauki kurtun man, ka zuba masa a ka, ka ce, ‘Ubangiji ya ce ya keɓe ka Sarkin Isra'ila.’ Sa'an nan ka buɗe ƙofa, ka gudu, kada ka tsaya.”
4 Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad.