1 Elisha kuwa ya kirawo ɗaya daga cikin annabawa matasa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kurtun mai, ka tafi Ramot-gileyad.
2 Sa'ad da ka isa can, sai ka nemi Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ka shiga, ka sa ya tashi daga wurin abokansa, ka kai shi cikin ɗaki.
3 Sa'an nan ka ɗauki kurtun man, ka zuba masa a ka, ka ce, ‘Ubangiji ya ce ya keɓe ka Sarkin Isra'ila.’ Sa'an nan ka buɗe ƙofa, ka gudu, kada ka tsaya.”
4 Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad.
5 Sa'ad da ya isa, sai ga shugabannin sojoji suna taro. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka, ya shugaba.”Yehu kuwa ya ce, “Wane ne a cikinmu?”Sai ya ce, “Kai ne, ya shugaba.”