16 Sa'an nan Yehu ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel, gama a can ne Yehoram yake kwance. Ahaziya Sarkin Yahuza ya gangara don ya gai da Yehoram.
17 Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezreyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa'ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.”Sai Yehoram ya ce, “Ka aiki wani, ya hau doki, ya tafi ya tarye su, ya tambaye su, ko lafiya.”
18 Sai wani mutum ya hau doki ya tafi ya tarye su, ya ce, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”Sai Yehu ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”Mai tsaro kuma ya ce, “Manzo ya kai wurinsu, amma bai komo ba.”
19 Ya kuma aiki wani, na biyu, a kan doki, ya je wurinsu ya ce musu, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”Yehu ya amsa, ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”
20 Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”
21 Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa'an nan Yehoram Sarkin Isra'ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel.”
22 Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?”Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?