4 Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad.
5 Sa'ad da ya isa, sai ga shugabannin sojoji suna taro. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka, ya shugaba.”Yehu kuwa ya ce, “Wane ne a cikinmu?”Sai ya ce, “Kai ne, ya shugaba.”
6 Sai Yehu ya tashi ya shiga ɗaki, saurayin kuwa ya zuba masa mai a ka, ya ce, “Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya keɓe ka sarkin jama'arsa, wato Isra'ila.
7 Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel.
8 Gama dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan datse wa Ahab kowane ɗa namiji, bawa ko 'yantacce, cikin Isra'ila.
9 Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yeroboam ɗan Nebat, da kuma kamar gidan Ba'asha ɗan Ahija.
10 Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa'an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.