7 Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel.
8 Gama dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan datse wa Ahab kowane ɗa namiji, bawa ko 'yantacce, cikin Isra'ila.
9 Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yeroboam ɗan Nebat, da kuma kamar gidan Ba'asha ɗan Ahija.
10 Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa'an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.
11 Da Yehu ya fita zuwa wurin sauran shugabannin, sai suka tambaye shi, “Lafiya kuwa, me ya sa mahaukacin nan ya zo wurinka?”Sai ya ce musu, “Ai, kun san mutumin da irin maganarsa.”
12 Suka ce, “Ba mu sani ba, sai ka faɗa mana.”Shi kuwa ya ce, “Ya faɗa mini, wai Ubangiji ya ce ya keɓe ni Sarkin Isra'ila.”
13 Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa'an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”