6 Rehobowam ya nemi shawara a gun dattawan da suke tare da tsohonsa Sulemanu, sa'ad da yake da rai, ya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa jama'ar nan?”
7 Su kuwa suka ce masa, “Idan za ka nuna wa jama'ar nan alheri, ka daɗaɗa musu rai, ka kuma yi musu magana mai daɗi, za su zama barorinka har abada.”
8 Amma ya ƙi yarda da shawarar da dattawan suka ba shi, ya nemi shawara daga wurin matasa waɗanda suka girma tare, masu yi masa hidima.
9 Ya ce musu, “Wace irin shawara za ku bayar wadda za mu amsa wa jama'an nan da suka ce mini, ‘Ka sawwaƙa mana wahalar da muka sha daga wurin tsohonka’?”
10 Sai matasa waɗanda suka girma tare da shi, suka ce masa, “Ga abin da za ka faɗa wa jama'an nan da suka ce maka, tsohonka ya tsananta musu, yanzu sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun ubana kauri!
11 Ubana ya tsananta muku ƙwarai, amma ni zan tsananta muku fiye da shi, ubana ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”
12 Sai Yerobowam tare da dukan jama'a suka koma wurin Rehobowam a rana ta uku, kamar yadda sarki ya faɗa, “Bayan kwana uku ku komo.”