12 Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.
13 Firistoci da Lawiyawa da suke a dukan Isra'ila kuwa suka komo gare shi daga dukan wuraren da suke.
14 Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da 'ya'yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji.
15 Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.
16 Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, daga kowace kabilar Isra'ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.
17 Sai suka ƙarfafa mulkin Yahuza, suka tsare mutuncin Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku. Suka yi shekara uku suna tafiya a tafarkin Sulemanu.
18 Rehobowam kuwa ya auri Mahalat 'yar Yeremot ɗan Dawuda, wadda Abihail 'yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.