15 Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.
16 Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, daga kowace kabilar Isra'ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.
17 Sai suka ƙarfafa mulkin Yahuza, suka tsare mutuncin Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku. Suka yi shekara uku suna tafiya a tafarkin Sulemanu.
18 Rehobowam kuwa ya auri Mahalat 'yar Yeremot ɗan Dawuda, wadda Abihail 'yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.
19 Mahalat ta haifa masa 'ya'ya maza, su ne Yewush, da Shemariya, da Zaham.
20 Banda Mahalat kuma, sai ya auri Ma'aka 'yar Absalom, wadda ta haifa masa Abaija, da Attai, da Ziza, da kuma Shelomit.
21 Rehobowam ya fi ƙaunar Ma'aka, 'yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. 'Ya'yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, 'ya'ya mata kuwa sittin.