3 Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat saboda ya bi halin tsohonsa da ya yi da fari, bai kuwa nemi Ba'al ba.
4 Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba.
5 Saboda haka ne Ubangiji ya ba shi ikon riƙon wannan mulki. Yahuza duka kuwa ta kawo wa Yehoshafat haraji, ya kuwa zama riƙaƙƙen mai dukiya, wanda kuma ake girmamawa.
6 Zuciyarsa ta ƙarfafa cikin al'amuran Ubangiji. Ya kawar da masujadai, da Ashtarot daga ƙasar Yahuza.
7 A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya aika da ma'aikatansa, su Ben-hail, da Obadiya, da Zakariya, da Netanel, da kuma Mikaiya don su yi koyarwa a biranen Yahuza.
8 Tare da su kuma akwai Lawiyawa, da Shemaiya, da Netaniya, da Zabadiya, da Asahel, da Shemiramot, da Jonatan, da Adonaija, da Tobiya, da Tob-adonaija, tare da waɗannan Lawiyawa akwai firistoci, Elishama da Yehoram.
9 Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari'ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko'ina a biranen Yahuza suka koyar da jama'a.