1 Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me'uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat.
2 Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat cewa, “Mutane masu yawan gaske suna zuwa su yi yaƙi da kai daga Edom, da kuma teku, har sun iso Hazazon-tamar,” wato En-gedi.
3 Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.
4 Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji.
5 Sai Yehoshafat ya tsaya a gaban taron jama'ar Yahuza da na Urushalima, a Haikalin Ubangiji, a gaban sabuwar farfajiya,
6 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.