3 Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.
4 Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji.
5 Sai Yehoshafat ya tsaya a gaban taron jama'ar Yahuza da na Urushalima, a Haikalin Ubangiji, a gaban sabuwar farfajiya,
6 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.
7 Ya Allahnmu, kai ne ka kori jama'ar ƙasan nan a gaban jama'arka Isra'ila, ka kuma ba da ita har abada ga zuriya masoyinka Ibrahim.
8 Suka kuwa zauna a cikinta, suka gina Wuri Mai Tsarki saboda sunanka cewa,
9 ‘Idan wani mugun abu ya same mu, kamar takobi, ko hukunci, ko annoba, ko yunwa, to, za mu tsaya a gaban wannan gida, a gabanka kuma, gama sunanka yana cikin gidan nan, idan mun yi maka kuka saboda wahalarmu, kai kuwa za ka ji, ka cece mu.’