25 Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.
26 Lawiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dawuda, firistoci kuwa suna riƙe da ƙahoni.
27 Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra'ila, suka kama.
28 Dukan taron suka yi sujada, mawaƙa suna ta raira waƙa, masu ƙahoni suka yi ta busa. Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa.
29 Bayan da an gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada.
30 Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.
31 Hezekiya kuwa ya amsa ya ce, “Yanzu dai kun tsarkake kanku ga Ubangiji. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a Haikalin Ubangiji.” Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, dukan waɗanda suka yi niyya kuwa suka kawo hadayu na ƙonawa.