2 Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo.
3 Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.
4 Hezekiya ya kuma umarci jama'ar da suke zaune a Urushalima su riƙa ba da rabon firistoci da na Lawiyawa, domin su mai da hankali ga dokar Ubangiji.
5 Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko'ina, sai jama'ar Isra'ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.
6 Jama'ar Isra'ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi.
7 A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai.
8 Sa'ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama'arsa Isra'ila.