29 Ya kuma giggina wa kansa birane, yana da garkunan tumaki da na awaki, da na shanu a yalwace. Gama Allah ya mallakar masa da abubuwa masu yawa.
30 Hezekiyan nan kuwa ya datse ruwan da yake gangarawa daga kogin Gihon, ya karkatar da su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dawuda. Hezekiya ya arzuta da dukan ayyukan da ya yi.
31 A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.
32 Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, ga shi, an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.
33 Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa'ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.