1 Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana mulki a Urushalima.
2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya yi irin ayyukan banƙyama da al'ummai waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban jama'ar Isra'ila suke yi.
3 Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba'al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu.
4 Ya kuma giggina bagadai a cikin Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima sunana zai kasance har abada.”
5 Ya giggina bagadai ga dukan rundunar sama a farfajiyan nan biyu na cikin Haikalin Ubangiji.
6 Ya miƙa 'ya'yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha'ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.