13 Su ne shugabannin masu ɗaukar kaya, suke kuma nuna wa kowane ma'aikaci irin aikin da zai yi, waɗansu daga cikin Lawiyawa, magatakarda ne, da ma'aikatan hukuma, da masu tsaron ƙofofi.
14 Sa'ad da suke fitowa da kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya gāno littafin Shari'ar Ubangiji wanda aka bayar ta hannun Musa.
15 Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari'a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin.
16 Shafan kuma ya kai wa sarki littafin, sa'an nan ya faɗa wa sarki cewa, “Dukan abin da aka sa barorinka su yi suna yi.
17 Sai suka juye kuɗin da aka samu don Haikalin Ubangiji, suka miƙa wa masu lura da aikin, da ma'aikatan.”
18 Magatakarda Shafan kuwa ya faɗa wa sarki, ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta wa sarki littafin.
19 Da sarki ya ji irin maganganun da littafin ya faɗa, sai ya yayyage tufafinsa.