37 duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, ‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,’
38 in sun tuba da zuciya ɗaya, a ƙasar da aka kai su, in sun fuskanci ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, suka yi addu'a, suna kuma fuskantar Haikalin nan da na gina domin sunanka,
39 sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu, daga wurin zamanka a Sama, ka sa su yi nasara, ka biya musu muradinsu, ka gafarta wa jama'arka waɗanda suka yi maka zunubi.
40 “Yanzu fa, ya Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kasa kunnuwanka, ka saurari addu'ar da ake yi a wannan wuri.
41 Yanzu fa, ya Ubangiji ka tashi ka tafi wurin hutawarka, kai da akwatin ikonka. Ya Ubangiji Allah ka yi wa firistocinka sutura da cetonka, adalanka kuma su yi farin ciki da nagartarka.
42 Ya Ubangiji Allah kada ka juya baya ga keɓaɓɓenka, ka tuna da madawwamiyar ƙaunarka ga bawanka Dawuda.”